Faifen Bidiyo: Hukumar Kwastam Ta Barranta Kanta Da Wasu Jami’an Ta Da Suka Dambata Da VIO.

Spread the love

Hukumar kwastam ta bayyana rashin jin dadin ta kan wani faifen bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, bayan ake zargin jami’an kwastam din sun farwa jami’an dake binciken ababen hawa ( VIO) a mahadar AYA dake birnin tarayya Abuja.

Faifen bidiyon ya nuna jami’an kwastam din sanye da kakinsu, suna kai duka da naushi tare da jin karar harbin bindiga, a ofishin jami’an VIO din kafin jami’an yan sanda su shiga tsakani.

Hukumar dai ta yi Allah Wadai da irin wannan rashin da’a da zubar da kimar aiki da jami’an ta suka yi da jami’an VIO.
Kakakin hukumar na kasa Nigeria, Abdullahi Mai Wada, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Talata.

Sanarwar ta ce za a gudanar da bincike tare da daukar matakin ladabtarwa don hana afkuwar hakan anan gaba.

“An ja hankalinmu kan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta,da ke nuna wasu jami’an hukumar kwastam ta Najeriya (NCS) a arangamar da suka yi da jami’an binciken ababan hawa (VIO).

jaridar idongari.ng, ta ruwaito cewa hukumar ba ta bayyana musabbabi abida ya sanya jami’an na ta zuwa ofishin jami’an VIO din tare cin zarafinsu ta hanyar duka da kuma duka harma da jin karar harbin bindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *