Farashin Kankara Ya Fadi Warwas A Birnin Kano

Spread the love

Farashin Kankara a birnin Kano, ya fadi warwas sakamakon yanayin hazo da sanyi da ake samu jifa-jifa wanda aka fara fusknata tun a mokon jiya.

A makon da ya gabata ana siyar da babbar Ladar Kankara akan naira 600 zuwa 700, inda ake siyar da Kakarar Ledar Pure water,kan naira 200 zuwa 300 sakamakon yanayin zafin rana da kuma bukatar ta a wannan lokaci na Azumin Ramadana.

Wani bincike ya tabbatar da cewa, yanzu haka ana siyar da karamar Ledar kankarar nairar 100 zuwa 150, ya yin da babbar Leda ake siyar wa kan naira 250.

Ma su siyar da kankarar da kan gudanar da harkokin kasuwancin da misalin karfe 3:00pm na rana zuwa 6:00pm wanda suka koka da rashin cinikiĀ  biyo bayan yanayin hazon da ake samu.

Wata mai sana’ar Kankara akan titin Katsina Road, Halima Aliyu, wadda ta dauki shekaru hudu tana gudanarwa, ta ce tana samun ribar naira 50 akan kowacce daya.

Najeriya ta jajanta wa Rasha kan harin da aka kai wani gidan rawa

Matsalar Tsaro Ta Sake Dawowa A Bauchi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *