Farashin Kayayyakin Masarufi Na Ci gaba Da Tashi A Najeriya

Spread the love

‘Ƴan Najeriya na ci gaba da kokawa bisa yadda kayayyakin masarufi ke ci gaba da tashi a kasuwannin kasar, duk da cewa darajar Naira sai kara samun tagomashi yake yi.

A baya, ‘yan kasuwa sun alakanta tashin farashin kayayyaki a kasar da yadda farashin kudin musayar Dalar Amurka yake a kasuwar canji, sai dai yanzu kusan makonni takwas, farashin Naira na dada samun tagomashi.

Idan za’a iya tunawa a baya, farashin na Dalar Amurka a kasuwar musayar canjin Najeriya, ya kai kusan Naira 2,000, yanzu kuma ana musayar Dalar Amurka a kasuwar musayar canjin akan kasa da Naira 1,400.

Zaidu Bala, shi ne shugaban kungiyar Muryar talaka a Najeriya, ya koka game yadda farashin kayaki ke ci gaba da tashi a kasuwannin kasar, duk da cewa farashin dalar Amurka na samun koma-baya a kasuwar musayar canji.

Shugaban na Muryar Talaka, ya ce “a baya ‘yan kasuwa sun ce tashin farashin dala ne ya ta’azzara tsadar kayaki a kasar, sai gashi yanzu farashin dalar faduwa yake tayi, amma farashin kayaki basa sauka.”

Bala ya dora alhakin rashin saukowar farashin kayaki a kasar, akan ‘yan kasuwa da kuma mahukunta, bisa rashin tsawatar wa da kuma daukar mataki akan masu ingiza farashin kayaki domin cin kazamar riba.

Nasiru Mato, Shugaban ‘yan kasuwa ne a jihar Yobe, ya daura alhakin tashin farashin kayayyakin akan masana’antun da ke kasar.

Nasiru, ya ce “masana’antun dake sarrafa nau’ukan kayakin masarufi da suka hada da Suga, Shinkafa da kuma Fulawa, a Najeriya basu sassauto da farashin su ba, sai dai kara farashin da sukayi a ‘yan kwanakin nan, duk da cewa farashin dala ya samu naƙaso a kasuwar musayar canji.”

A hirarsa da Muryar Amurka, Dakta Isa Abdullahi Kashere manazarci kuma masanin tattalin arziki a Jami’ar Tarayya dake Kashere Jihar Gombe, ya ce faduwar Darajar Dalar Amurka a kasuwar musayar canji, ba zai sauko da farashin kayaki a kasar nan take ba, ganin cewa ‘yan kasuwa da masana’antu a kasar, sun sayi kayakin nasu a lokacin da dalar Amurka ke da tsada.

Dakta Kashere, ya kara da cewa wasu yan kasuwan na kara farashi ne nan take da zaran sunji dalar ta tashi, amma yanzu da dalar ta samu koma baya, ‘yan kasuwar ba zasu karyar farashin ba, saboda gudun asara.

Yanzu yan Najeriya dai na dakon ganin irin matakan da gwamnatin tarayya zata bijiro dashi domin ganin farashin kayaki sun sauko a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *