Fashewar wani abu ya janyo ruɗani a Ibadan

Spread the love

Fashewar wani abu ya janyo ruɗani a Oyo, babban birnin jihar Ibadan.

Fashewar da ta faru a yammacin Talatan nan, ta ruguza gine-gine da dama saboda mummunar jijjiga.

Kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun ruwaito cewa motoci da gidaje sun tarwatse a yankunan Awolowo, Bodija, Akobo da kuma sauran yankuna.

Sai dai har yanzu ba a kai ga tabbatar da yawan waɗanda suka jikkata ba a lamarin.

A wani sako da ta wallafa a shafin X, gwamnatin jihar ta Oyo , ta ce ta samu labarin fashewar da ta afku a jihar.

Gwamnatin ta buƙaci mazauna jihar da su kwantar da hankali yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike domin gano abin da ya janyo fashewar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *