Tsohon kwamishinan aiyuka na musamman na jahar kano, Hon. Muntari Ishaq Yakasai, ya magantu kan wasu Festocinsa da hotuna wadanda suke yawo a shafukan sada zumunta, da nufin neman kujerar shugabancin jam’iyar APC reshen jahar Kano.
Muntari Yakasai , ya ce ganin hotunansa a jikin Festoci ba komai ba ne, sai fatan Alkairi da wasu bayin Allah suke yi masa.” Fatan alkairi ne wasu bayin Allah suke yi mun, saboda haka ba zaka hana mutane yin hakan ba” Muntari ishaq”.
Tsohon kwamishinan ya bayyana hakan ne a jiya Asabar , lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai, bayan kammala taron kaddamar da na’urori masu kwakwalwa da kungiyar daliban Yakasai ( YAKSA) ta shirya a birnin Kano kamar yadda jaridar idongari ta ruwaito.
Yakasai ya yi wa kungiyar Daliban godiya bisa yadda suke da burin nema matasa makoma mai kyau ta hanyar koyar Na’ura mai kwakwalwa, don samun sana’o’in da za su dogara da kansu.
Kungiyar Daliban ta ce ta samu tallafi ne daga masu ruwa da tsaki na unguwar Yakasai, don ci gaba da horas da daliban na’ura mai kwakwalwa don su yi gogayya da takwarorinsu na sassan duniya.
- Mai Ba Wa Gwamnan Kano Shawara Kan Ilimin Yaya Mata Hafsat Adhama Ta Ba Da Tallafin Kayan Karatu A Gwale
- SEDSAC ta Yabawa Gwamnan Kano Bisa Nadin Waiya Da Iro Ma’aji A Matsayin Kwamishinoni