Festulation Foundation ta koyar da mata 50 sana’o’in dogaro da kai bayan sun warke daga larular yoyon fitsari a Kano

Spread the love

Cibiyar kula da masu larular yayon fitsari ta Festula Foundation of Nigeria, ta yi wa mata 50 aiki kyauta tare da horas da su, sana’o’in dogaro da kansu bayan sun koma gida.

Matan da aka koyar da su sana’o’in na daga cikin matan da Festula Foundation, tare da hadin kan ma’aikatar mata ta jahar Kano, suka kula da lafiyar su har suka warke a cibiyar dake Unguwar Kwalli Kano.

Shugaban cibiyar Festula Foundation, Musa Isa, (Baba Musa) , ya bayyana damuwarsa ga me da yanayin da masu fama da larular ke tsintar kansu sakamakon tsangwamar da wasu mutane ke yi .


Musa Isa ya kara da cewa, bayan samun masu fama da cutar sun nemi izini daga ma’aikatar mata da kananan yara ta jahar Kano, don su yi musu Tiyata kyauta har suka warke, sannan suka koyar da su sana’o’in da kowacce daga cikin su ta zaba da kanta.

Wasu daga cikin sana’o’in da aka horas da su , sun hada, Dinki, Gurguru, Kiwon Awaki da sana’ar kulikuli da kuma Gurasa da daidai sauransu.

Ya kara da cewa, sun bayar da kekunan dinki 20, injinan markade 2, buhunan gyada, buhunan Fulawa, tukwanen yin Gurasa da kuma naira dubu arba’in arba’in ga wadanda suka zabi sana’ar Kiwon Awaki.

An rantsar da Ododo a matsayin sabon gwamnan Kogi

” Mun hada gwiwa da ma’aikatar mata muka koyar da su sana’o’i daban daban, a wannan gida na Kwalli tsawon sata shida” Baba Musa”.
Cikin wadanda suka amfana da tallafin sun hada da yan jahar Kano, Maiduguri, Ibadan, Jigawa, Katsina da daidai suaransu.
” Macen da ta kamu da larula ta warke tana cikin farin ciki kuma zata koma gida da kayan sana’a wannan shi zai sa ta samu daukaka da kulawa a gida” Baba Musa”.

Akarshe Baba Musa ya yi kira ga gwamnati, tasan cewar duk duniya, duk macen da ta kamu da cutar yoyon fitsari kamar yadda Majalissar dinkin duniya ta zartar cewa a tabbatar an yi mata aiki kyauta.

Sai da ya ce a jahar Kano abun ba haka yake ba, domin kayan aikin da yakamata a tabbatar an bayar don yi wa mace aiki kyauta babu su a cibiyar da ake aikin yoyon fitsarin a asibitin Murtala Muhammed.


” Wannan kalubale ne babba kuma, mu akoda yaushe muna tanadar kayan da ake bukata ba tare da masu fama da larular sun siya ba” Babba Musa”.
Inda ya dada kiran gwamnatin jahar Kano ta tanadi kayan irin wannan aiki da za a dinga yi wa mata aiki kyauta.


Da take karin bayani kwamishiniyar ma’aikatar mata ta jahar Kano, Dr. A’isha Lawan Saji, waddda babbar sakatariya a ma’aikatar Dr. Sa’adatu Sa’idu Bala, ta wakilta ta bayyana cewa cibiyar tana karkashin gwamnatin jahar Kano, kuma dukkan abubuwan da ake bukata suna samar mu su ciki harda abinci da sabulun wanki da na wanka.

Dr. Sa’adatu Sa’idu ta kara da cewa, masu lalurar na shan tsangwama, amma dai gwamnati na fadakar da su.

Kano: Hukumar KAROTA ta musanta wani rubutu da ta gani yana yawo da sunan ta

Haka zalika ta yi kira ga al’umma su daina kyamar ma su, fama da laruwar , sannan ta gargadi matan su rike sana’ar da suka koya.

A karshe ta yaba wa Festula Foundation, bisa namijin kokarin da ta ke yi a koda yaushe, don fitar da mata daga kuncin larular da suke fama da ita, harda koyar da su sana’o’in dogaro da kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *