Fintiri ya haramta rufe lambar motocin gwamnati a Adamawa

Spread the love

 

Gwamna Adamawa Ahmadu Fintiri ya haramta wa jami’an gwamnati rufe lambobin motocinsu yayin tuki a kan titunan jihar.

Wannan mataki dai na da nufin hana wasu mutane da ke da mugun nufi yin kamanceceniya da jami’an gwamnati ta hanyar yin amfani da lambar mota da aka lullube wajen gudanar da ayyukan laifi.

Gwamna Fintiri ya bayyana hakan ne bayan ya karbi lambar yabo na gwaninta a matsayin gwamna fi kula da jinsi daga matan jihar Adamawa suka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *