Gidauniyar Fistula Foundation Nigeria, wadda ke tallafawa mata masu fama da lalurar yoyon fitsari, ta gudanar da taron yaye mata 50 da aka yi mu su aikin gyara kyauta, tare da raba musu kayan sana’o’i domin su dogara da kansu.
Taron, wanda aka shirya a harabar cibiyar kula da masu fama da lalura yoyon fitisari dake Unguwar Kwalli Kano, ya samu halartar jami’an gwamnati, wakilai daga ƙasashen waje, da ƙungiyoyi masu zaman kansu.
Mrs Pharma Loney ita ce shugaban gidauniyar Fistula Fundation ta duniya wadda ta zo daga kasar Amurika ta yaba da yadda ake kula da masu fama da lalurar.
Shugaban Gidauniyar, Musa Isah, wanda aka fi sani da Baba Musa, ya bayyana cewa manufa ta shirya wannan biki ita ce nuna farin cikin nasarar da suka samu wajen taimaka wa mata da ke fama da yoyon fitsari ta hanyar yi musu aiki kyauta da kuma samar musu da kayan dogaro da kai.
“Makasudin wannan shiri shi ne mu ga waɗannan mata sun dawo cikin koshin lafiya, kuma sun samu damar dogaro da kansu ta hanyar sana’a. Wannan lalura tana lalata rayuwar mata da dama, amma muna ƙoƙarin dawo da martabarsu,” in ji Baba Musa.
kungiyar ce ta gyara dukkan gidan da maatn suke tare da sanya masa gadaje da samar da wajen koyar da sana’a harma da dakin duba lafiyarsu.
- Zanga-zanga- Kungiyar Lauyoyi Mata Ta Yi Kira Ga Sufeton Yan Sandan Nigeria Kar Ya Amsa Kiran Sauya CP Ibrahim Bakori Daga Kano
- Yan Sandan Kano Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da aikata Laifuka Mabambanta
Baba Musa ya ƙara da cewa gidauniyar ta samu nasara wajen inganta cibiyar kula da masu yoyon fitsari da ke Kwalli, wanda hakan ya sauƙaƙa aikin kula da lafiyar mata masu fama da wannan matsala.
“Mun gyara cibiyar tare da samar da kayan aiki na zamani da ƙwararrun ma’aikata, domin tabbatar da cewa mata da yawa sun samu kulawa mai inganci,” in ji shi.
Wakilin Kwamishiniyar Ma’aikatar Mata ta Jihar Kano, Malam Muhammad Sabo Iliyasu, ya yaba da ƙoƙarin gidauniyar bisa gudunmawar da take bayarwa wajen dawo da martabar mata masu fama da yoyon fitsari.
“Wannan aiki abin yabawa ne sosai. Gidauniyar tana taimaka wa mata da suka yi fama da wannan matsala tsawon shekaru, sannan tana ba su kayan sana’a domin su fara sabuwar rayuwa cikin ƙima da mutunci,” in ji Sabo.
Matan an raba musu Kekunan Dinki, injinan markade, injin yin gurguru da dai sauransu.
Taron ya gudana cikin farin ciki da nuna godiya daga waɗanda suka amfana, inda da dama daga cikinsu suka bayyana cewa tallafin ya ba su damar sake tsayawa da kafafunsu bayan dogon lokaci na wahala da ƙunci.