Hukumomi a Taiwan sun tabbatar da maƙalewar mutum 127 cikin ɓuraguzan gini sakamakon girgizar ƙasar da ta faru.
Cikin adadin, 77 a cikinsu sun maƙale a cikin wata hanya da ke ƙarƙashin tsauni a Jinwen da Daqinqshui a Hualien, kamar yadda jami’ai suka bayyana.
Sannan mutane biyu Jamusawa ne da suka maƙale a hanyar ƙarƙashin ƙasa a Chongde da ke gandun daji na yankin.
Sauran mutum mutum 50 kuma sun maƙale a ƙananan motocin bas huɗu da suke hanyar zuwa gandun dajin Taroko daha birnin Hualien.
Dukkansu ma’aikata ne da za a kai otal ɗin SilksPlace Taroko gabanin hutun yini huɗu daga Alhamis zuwa Lahadi.