Aƙalla fursunoni 118 ne suka tsere daga gidan yarin Suleja da ke jihar Naija mai maƙwabtaka da birnin Abuja, sakamakon ruwan sama mai kama da bakin ƙwarya da ya ruguza wani ɓangaren ginin gidan ranar Laraba.
Mai magana da yawun hukumar gyaran hali ta birnin Tarayya, Adamu Duza, a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis ya ce “sakamakon ruwa kamar da baƙin ƙwarya da ya kwashe awa 24 yana zuba ya lalata wasu sassan gidan yarin inda fursunoni 118 suka tsere.”
To sai dai wani jami’in gidan yarin da BBC ta tattauna da shi ya ce kawo yanzu an samu damar kama fursunonin 10 daga cikin 118 ɗin da suka tsere, inda kuma suke ci gaba da baza komar neman mutum 108.
- Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da Yin Amfani Da Ankwa Suna Kwacen Wayoyi A Adaidaita Sahu A Kano.
- Matar da ke fafutukar taya mutane su kashe kansu ta mutu