Fursunoni 58 Ne Ke Rubuta Jarrabawar NECO A Kano

Spread the love

Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta kasa reshen jihar
Kano   ta   sanar   da   cewa   fursunoni   58   ne   suke   rubuta
jarabawar NECO a wannan lokaci.

Kakakin hukumar Musbahu Kofar Nasarawa ne ya sanar
da hakan cikin wata sanarwa daya fitar .

Kakakin hukumar Ya ce an cimma wannan nasara ce bayan da gwamnatin jihar Kano ta biya kudin jarabawar fursunonin.

Kakakin hukumar Ya bayyana cewa wannan kokari da gwamnati ta yi alamu ne, na kudurin ta na inganta rayuwar mazauna gidajen gyaran halin.

Hukumar ta bayyana godiya ga gwamnan Kano bisa biyan kudin jarabawar mazauna gida yarin wanda ya ce wannan zai taimaka wajen karfafa musu gwiwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *