Fursunoni da dama sun tsere daga gidan yarin Nija

Spread the love

Hukumomi a Nijar sun saka dokar hana fita a yankin Tillaberi bayan fursunoni da dama sun tsere daga wani gidan yari mai tsananin tsaro kuma da ke tsare da masu iƙirarin jihadi.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis lokacin da mutanen suka gudu daga gidan yarin na Koutoukale mai nisan kilomita 50 daga Yamai babban birnin ƙasar, in ji ma’aikatar harkokin cikin gida ta Nijar.

An yi nasarar daƙile yunƙurin ɓalla gidan yarin a 2016 da kuma 2019.

Dakarun sojin Nijar na fama da hare-haren masu iƙirarin jihadi a yammacin ƙasar, a gefe guda kuma suna kare aikin shugabanninsu da ke mulki bayan juyin mulkin da Janar Tchiani ya jagoranta a shekarar da ta gabata.

Ma’aikatar ba ta fayyace yawan fursunonin da suka gudu ba a lamarin na jiya.

Sai dai kuma ana fargabar cikin waɗanda suka tsere akwai mayaƙa na ƙungiyoyin al-Qaeda da Islamic State.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *