Ga jerin sunayen yan daba 72 da Rundunar yan sandan Kano ke nema ruwa a jallo

Spread the love

 

Rundunuar yan sandan jahar Kano, ta shelanta neman wasu matasa 72 da ake zargi da aikata laifukan daba a yankin karamar hukumar Dala.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel ne, ya bayyana hakan ya yin zantawarsa da Idongari a shelkwatar rundunar a ranar juma’a.

CP Gumel, ya ce wadanda ake zargin suna fito wa ne domin gungun-gungu, da suke tsoratar da al’umma dan su aikata mu su fashi.

Yansanda sun kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja

Sai dai ya kara da cewa, makonni biyu kenan da fara samun labarin gungun matasan, da suka fito da wani sabon salo dan razanar da jama’a ta hanyar wasa wukake a kan tituna su firgita jama’a su gudu gidajen su ,sannan su aikata mugun nufunsu na sace-sace dai dai sauransu.

Yan sanda sun ce sun gano wani da ya mika kansa a baya, a yanzu yana jagorantar gungun wasu matasa suna tayar da hankalin mutane a unguwanni da dama ciki har da yankin Dala.

Cikin jerin sunayen da rundunar ta fitar sun hada da:

 

   No Sunaye Unguwa
1. Bahago Afah Kuka Bulukiya
2. Malam Keya Dogon Nama
3. Habu Mayo Kuka Bulukiya
4. Dan Mama Adakawa
5. Alhajin Bilal Lungun B/malam Madabo
6. Buda Karofin Dala
7. Alhaji Baba Shirawa
8. Abba Gashi Gashi Dandinshe Tasha
9. Hassan Cisse Rijiya Biyu
10. Dan Kamsusi Dandinshe
11. Likuman Makafin Dala
12. Saddiku Style Gadar Salga
13. Kwaja Dandinshe
14. Malam Rodi Dala Makarantar Nafahatu
15. Halifa Dan Asabe Shatsari
16. Bagiya Shatsari
17. Abba Ali Mugu Sanka
18. Dan Kyahun Rijiya Biyu
19. Nabara’u Madigawa
20. Habu Udukul Madigawa
21. Fato Madigawa
22. Haruna Musa Jibrin Madigawa
23. Malam Shehu Madigawa
24. Dahuwa Chediya
25. Fiya Dandinshe
26. Dubulliya Aikawa
27. Sharu Sharna Rijiya Biyu
28. Bukari Tijjani Dala
29. Dan Auwalu Kwanar Dala
30. Dan Chaina Kul-kul
31. Shangwa Rimin Abba Kul-kul
32. Dan Yellow Chediya
33. Abba Kan Fulogi Rijiya Biyu
34. Dilin Dala Layin Sarka Gurgu
35. Dandolo Lungun Kotu
36. Master Lungun Kotu
37. Dogo Kantin Uba Angwaye Titin Alfanda
38. Bala Kwalli Kantudu
39. Ala Baka Bakin Kasuwa Maskwani
40. Ummo Lungun Kotu
41. Walidi Lungun Yankifi
42. Guguwa Yalwa
43. Bisi Yalwa
44. Yartakabiruwa Yalwa
45. Ubaidu Kantudun Madabo
46. Shatoli Filin
47. Dan Isa Shirawa
48. Kabiru KB Show Bayan Dala Lungun Nafahatu
49. Nurere Lungun Kotu
50. Abba Ho Filin Faroma
51. Saddiku Savio Filin Kutare
52. Wando Filin Kutare
53. Yahaya Army Lungun Nafahatu
54. Mubarak Bade Lungun Nafahatu
55. Dan Umar Ziri Zirin Gyaranya
56. Abdul Lokon Makera Shatari
57. Addahir ( Dahri) Dirimin Daje
58. Tere Dirimin Daje
59. Annani Karofin Daganda
60. Tata Kantudu
61. Dan Sani Falo
62. Oris Kantudu
63. Tsulum Lungun Kankarofi
64. Mamman Kantudu
65. Malo Kantudu
66. Al-amin Makafin Dala
67. Tulu Dala
68. Abba Idan Dala
69. Tahani Lungun Yan Kifi
70. Kilo Dala
71. DaN Jamilu Adakawa
72. Dan Turkwi Adakawa

 

Kwamishinan ya ce, wannan ba fadan daba ne kamar yadda aka sani abaya domin har yanzu babu wanda aka jiya wa rauni, ko aka kwantar dashi asibiti, kawai suna yi ne domin tayar da kura su aikata laifin fashi , da kuma farfasa motocin jama’a da dai sauransu.

Ya kuma ce matasan da suke fitowa suka aikata fashin rundunar ta tabbatar da cewa masu laifi ne, domin za su shiga farautar su.

CP Gumel, ya umarci jami’an yan sanda tare da shawartar yan bijilanti da masu unguwanni duk inda suka gansu su cafke su dan gurfanar da su a gaban kotu.

Kwamishinan ya ce wannan lokacin ba na yin afuwa ba ne lokaci ne na yin fito-na fito da su duk inda aka gansu.

Kotu ta aike da yar Tiktok Ramlat Princess gidan gyaran hali bisa zargin yada badala

Yansanda sun kama mutum takwas da suke zargi da sace ɗaliban Ekiti

A karshe kwamishinan ya yi kira ga iyaye da su dinga tsawatarwa da yayan su a duk lokacin da suka gansu da wani makami su karbe shi tare da yi musu nasiha kan illar dake tattare da rike makami ba tare da samun izini ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *