Ga Wata Sanarwa Daga Rundunar Yan Sandan Jahar Kano

Spread the love
Bompai Logo

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, sashin kwantar da tarzoma za su gudanar da atisayen harbin Bindiga daga ranar Alhamis 5 ga watan Satumba zuwa juma’a 6 ga watan Satumba 2024.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labari a daren Talata nan.

Ya ce Yan Sandan kwantar da tarzoma Mai 52 dake Challawa , sune za su gudanar atisayen harbin Bindigar, a kebantaccen wurin nan hawan Kalebawa, dake karamar hukumar Dawakin Tofa.

SP Abdullahi Kiyawa ya kara da cewa za a fara atisayen harbin tun daga karfe 6:00am zuwa 6:00pm na yammacin ranakun.

Idongari.ng, ta ruwaito cewa kwamishinan yan Sandan jahar CP Salman Dogo Garba, ya shawarci mazauna yankin musaman , Danbazau, Gangaren Dutse, Tumfafi, Kakurum da Dandalan dake kananan hukumomin, Dawakin Tofa da kuma Ungoggo, da su kauracewa wajen kuma kar su firgita dajin karar harbin da za suji har sai an kammala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *