Ga Wata Sanarwa Daga Rundunar Yan Sandan Kano

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Kano tana sanar da daukacin al’umma cewa jami’an rundunar yan sanda mai lamba 52 (PMF) Squadron dake Challawa Kano za su gudanar da atasayen harbi na kwanaki biyu a Hawan Kalibawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano , da misalin karfe 6 safe zuwa 6 na yamma daga ranar Asabar, 11th da Lahadi 12th ga watan Mayu 2024.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Sanarwar ta shawarci jama’a musamman mazauna kauyukan Dambazau, Gangaren Dutse, Tumfafi, Kakurum da Dandalama a kananan hukumomin Dawakin Tofa da Ungogo da kewaye da su nisanta daga wajen, kuma kada su firgita da karar harbin atasayen da zasu gudanar.

Kwamishinan yan sanda CP Mohammed Usaini Gumel, FIPMA, psc, ya yabawa alummar jihar Kano bisa fahimtar juna, addu’oi, goyon baya da hadin kai da suke baiwa rundunar a koda yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *