Gabashi da Kudancin Afirka ne suka fi yawan masu cutar HIV – Rahoto

Spread the love

Wani sabon bincike da Hukumar yaƙi da cutar HIV ta Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar ya nuna cewa ana samun bambanci a yadda ake yaƙi da cutar Sida a duniya.

Rahoton ya ce ƙasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara ne ken kan gaba wajen yaƙi da cutar yayin da sauran ɓangarorin duniya ke biye mata a baya.

Yawan mutanen da ke kamuwa da cutar HIV ya ragu da fiye da kashi 50 cikin 100 tun daga shekarar 2010.

Shugabar shirin yaƙi da cutar HIV ɗin ta MDD, Winnie Byanyima ta ce an samu nasarar ne sanadiyyar tsarin da ƙasar Afirka ta Kudu ta gabatar na yaƙi da cutar, wanda shi ne mafi girma a duniya.

Sai dai ta ce haramta ayyukan mata masu sana’ar karuwanci da kuma ƙyamar da ake nuna wa masu alaƙar jinsi ɗaya da masu sauya jinsinsu na asali ya haifar da ƙaruwar yaduwar cutar a nahiyar Turai da Tsakiyar nahiyar Asiya.

Har yanzu ƙasashen gabashin Afirka da ka Kudancin nahiyar ne suka zamo waɗanda cutar ta fi yi wa illa, inda sama da mutum miliyan 20 ke rayuwa da cutar ta HIV.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *