Gabon na Kada ƙuri’ar raba gardama don amincewa da sabon kundin tsarin mulki

Spread the love

Ƙasar Gabon na gudanar da ƙuri’ar raba gardama domin amincewa da sabon kundin tsarin mulki, wanda ake gani a wani mataki na mayar da ƙasar tafarkin Dimokraɗiyya.

Shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Brice Oligui Nguema – wanda ya kawo ƙarshen mulkin iyalin gidan Bongo na tsawon shekara gomman shekaru – ya alƙawarta mayar da mulki zuwa farar hula cikin shekara biyu.

Wasu goyon bayan sabon kundin tsarin mulkin sun bayyana matakin a matsayin wani mataki na sabunta makomar ƙasar, bayan tsawon shekara 50 na mulkin iyalan gidan Bongo.

Amma masu suka na cewa an tsara sabon kundin tsarin mulkin ta yadda zai taikama wa masu mulkin ƙasar, inda suke gargaɗin hakan ka iya haifar da mulkin mulaka’u.

Sabon kundin tsarin mulkin ya tanadar wa shugaban ƙasa wa’adin mulkin biyu na shekara bakwai-bakwai.

Haka kuma akwai wasu sabbin dokokin da suka shafi asali da za su iya hana hamɓararren shugaban ƙasar Ali Bongo tsayawa takara – saboda ya auri wata Bafaranshiya – kuma hakan zai iya hana ‘ya’yansa tsayawa takara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *