Gadar Sabon Titi Da Makotan Unguwanni Na Cikin Barazana A Daminar Bana.

Spread the love

 

 

Mazauna unguwannin, da suke daura da gadar karkashin kasa ta sabon titin zuwa Madobi a jihar Kano sun roki gwamnatin jihar data takawa wasu mutane burki kan yunkurin toshe magudanan ruwa , wanda suke ce hakan haifar da ambaliyar ruwa.

Sun ce yanzu wasu mutane sun fara aiki a ragowar filin gwamnatin tarayya da kuma wani bangare na gwamnatin Kano, wanda aka ware daga jikin titunan da ake yi a kusa da wajen.

Haka zalika masu ababen hawa suma sun bayyana damuwarsu kasancewar duk damina gadar ta ciki da ruwa wanda yake tahowa daga unguwannin, Ja’en , Sharada, Chiranci, Dorayi, da sauransu amma mutanen sun fara rufe hanyar ruwan data fito daga cikin gadar.

Tuni dai hukumar yaki da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta sanya alamar dakatar da aikin amma duk da haka ana ci gaba da yin aikin.

Wasu rahotanni na cewa masu aikin na ta kokarin ganin sun cire manyan falafalan wutar lantarkin da suke wajen tare da chanjawa hanyar ruwan waje .

Mazauna yankin da kuma masu ababen hawa da suke bin hnyoyin sunce yin wannan aiki zai haifar da ambaliyar ruwa ciki kuwa harda barazanar rushewar gadar baki daya domin ruwan bai samu hanyar wucewa ba kamar yadda aka tsara ta.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *