Ɗan Majalisar Tarayya daga Jihar Filato, Yusuf Gagdi ya gwangwaje ‘yarsa, Aisha Yusuf Gagdi da danƙareriyar motar ƙirar SUV a matsayin tukuici bayan ta kammala makarantar sakandare ta Lead British International a Abuja.
An ruwaito cewar Aisha, ta samu kyakkyawan sakamako a Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a (JAMB), wanda hakan ya sanya mahaifin nata yi mata bazata da kyautar mota.
Ɗan majalisar ya wallafa hotunan bikin kammala makarantar ’yar tasa a shafinsa na Instagram a ranar Asabar.
“Yau, na halarci bikin kammala makarantar ’yata. Kallonki ’yata kina tafiya kan dandali ya cike zuciyata da farin ciki da soyayya.
- NDLEA ta bankaɗo masu safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya
- Kotun ƙoli ta haramta ware guraben aiki ga keɓaɓɓun mutane a Bangaldesh
Na yi farin ciki da nasararki da kuma ƙwazon da kika nuna. Ina fatan ki ƙare hakan a gaba da farin ciki.
“Ina taya ki murna, tauraruwata mai haske!”
Sai dai kyautar motar da Gagdi ya bai wa ’yarsa ya bar baya da ƙura a kafafen sada zumunta.
Wasu na ganin bai kamata a ce an bai wa yarinya kyautar mota saboda ta kammala makarantar sakandare ba.
Wasu na ganin bai kamata ya bayyana kyautar ba duba da halin ƙunci da ake fama da shi a ƙasar nan.