Gamayyar Dalabai Yan Asalin Kano Sun Kaddamar Da Kwamitin Shirya Zaben Shugabanni.

Spread the love

Kungiyar Dalibai yan asalin jahar Kano, ta koka samakon fada wa mawuyacin hali tsawon shekaru hudu da Suka gaba ta ba tare da shugabanci ba.

Shugaban Gamaiyar dalibai yan asalin jahar Kano, wadanda suke karatu a sassa Nigeria da kuma ketare, Sanata Adamu Magaji Rabi’u Garin-danga, daga jami’ar Kimiyya Da Fasaha Ta Aliko Dangote Wudil Kano, ne ya bayyana hakan ya yin kaddamar da kwamitin da zai jagoranci yadda za a shirya sabon zabe cikin makonni uku ma su zuwa.

Magaji Rabi’u Garin-danga , ya ce yan kwamitin za su gudanar da aikin su ba dare ba Rana, kuma an zabo su ne sakamakon gogewarsu wajen tafiyar da harkokin dalibai.

Kwamitin ya zabi, Kwamared Usman Sani Shau’aibu Mai Dala, a matsayin shugaba, Abubakar Murtala Garba a matsayin Sakatare da Abdulganiyu Shehu Dalhatu a matsayin mai magana da yawun kwamitin sai kuma A’isha Ibrahim Aliyu, wadda aka Nada ta Ma’ajin kwamitin tsara zaben.

Sauran Mambonin kwamitin sun hada da, Baraya Hassan Garba, Abubakar Sa’ad Adam, Abdullahi Garbi Amna, Umar Abdulkadir Koguna, Yusuf Idris Garba, Yahya Shu’aibu Ahmed, Khadija Ado Ali, Umar Labaran Labson.

Sai kuma Muhyiddin Sulaiman Boka, Abdullahi Garba Muktar, Nafi’u Yunusa Aminu, Fatima Mustapha Bala, Muktar Shu’aibu Yusuf, Mubarak Sani , Mubashshir Tafida Tijjani, Zaharaddin Sani Abdullahi da kuma Fauziyya Abdulkadir Abubakar duka a matsayin mambobi.

Garin-danga ya ya bawa gwamnan jahar Kano, Engineer Abba Kabir Yusuf, bisa kokarin da yake yi kan Dalibai yan asalin jahar Kano, wadanda suke karatu a gida da kuma kasashen ketare.

” Ba shakka wannan gwamnati ta yi abunda tarihi ba zai manta ba , kan harkar ilimi domin shekaru 8 kenan ba a yi irin sa ba” Magaji Rabi’u Garin-danga “.

Ya Kara sa godewa gwamnan jahar , a madadin sauran daliban jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *