Gamayyar hukumomin tsaro a Kano sun tattauna da shugabancin jam’iyun siyasa gabanin zaben cike gibi da za a sake yi a Kunchi/Tsanyawa.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano tare da sauran hukumomin tsare da ke aiki a jahar,sun gudanar da wata tattauna wa da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC reshen jahar Kano, da kuma ma su ruwa da tsaki na shugabancin jam’iyyun siyasa, domin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya kan zaben cike gibi na dan majalissar dokokin jahar Kano,  da za a gudanar a karamar hukumar Kunchi da Tsanyawa.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan ga jaridar Idongari.ng, a ranar Talata.

A ranar 3 ga watan Fabararun 2024 , hukumar zabe mai zaman kanta, ta kasa reshen jahar Kano, ta dakatar da zaben karamar hukumar Kunchi, biyo bayan yadda wasu yan daba suka tarwatsa kayan zaben da yunkurin farwa jami’an INEC.

Kwamishinan zaben jahar Kano, Ambasado Abdu Zango, ya bayyana cewa, yan dabar sun kwashe kayan zaben, wanda hakan ya sanya su, suka je da gamayyar hukumomin tsaro , suka taho da ma’aikatan zaben domin tseratar da lafiyarsu.

Ambasada Abdu Zango

 

CP Gumel, ya ce a matsayin su na hukumomin tsaro sun amince cewar suna da isassun ma’aikata da kuma kayan aikin tabbatar da tsaro domin ganin an gudanar da zaben cike gibin ba tare da tashin hankali ba.

Kwamishinan yan sandan ya kara da cewa, hukumar zabe INEC ta tabbatar mu su cewar sun shirya dukkan kayan aikin da ake bukata wadanda za a yi aikin zaben da su.

‘’ Kawai abunda INEC ta ke bukata shi ne yarjejeniyar matakan da za mu dauka don tabbatar da an yi komai cikin kwanciyar hankali sabanin abunda ya faru a wancan lokaci da ba a karasa zaben karamar hukumar Kunchi ba’’ CP Gumel’’.

Kwamishinan yan sandan Kano, CP M.U. Gumel, ya karamar hukumar Kunchi ta na da akwatunan zabe 10, wadanda kwata-kwata zaben ma ba a yi shi ba, saboda kawai an wayi gari kusan yan tada zaune tsaye sun hana gudanar da zaben.

CP MUHAMMED USAINI GUMEL

‘’ A yanzu mun shirya tsaf a matsayin mu na jami’an tsaro’’ Gumel’’.

Hakan dai ya ba mu damar kiran ma su ruwa da tsaki na jam’iyun APC da NNPP da kuma sauran jam’iyu domin su zama shaida kan abunda muke yi , wadanda har suka yi Allah wadai da abunda ya faru a baya.

Hukumar kwastam ta Najeriya za ta raba kayan abincin da aka kama a faɗin ƙasar

Ƴan sandan Najeriya sun tarwatsa gugun ƴan bindiga a jihar Anambra

Sai dai ya ce jam’iyyun sun tabbatar mu su cewar duk wanda aka gani da makami ya yi gaban kansa ne, babu ruwan jam’iya, jami’an tsaro su kama shi don yi masa hukunci.

Kwamishinan yan sandan ya kara da cewa daga cikin matakan da suka dauka shi ne, karamar hukumar Kunchi, daga 12 daren jajiberen ranar zaben da za a sanya , nan bada jima wa ba, babu shiga babu fita, don tabbatar da tsaro.

Ya ce duk dan siyasar da yake da mukamin gwamnati ba a yarda ya shiga harkokin zaben ba , ko zuwa don duba rumfunan zabe.

‘’ don haka idan kai jami’in gwamnati ne babu wani dalili na zuwan ka rumfar zabe.

‘’duk wani mai mukami ya tsaya inda yake ya kama kansa , matukar ba shi da kuri’ar da zai kada domin idan jami’an tsaro suka kama shi sunan sa mai dagula kuri’a’’ CP Gumel’’.

CP Muhammed Gumel ya ce babban farin cikin su shi ne a yi zaben lafiya ba tare da an zubar jinin wani ko tashin hankali ba.

Kwamishinan hukumar zaben reshen jahar Kano, Ambasada Abdu Zango, hukumomin tsaro sun tabbatar mu su za su samar da ingantaccen tsaro, ya yin da jam’iyun siyar kuma suka amince da yarjejeniyar sanya hannu na zaman lafiya .

Abdu Zango ya kara da cewa a baya an samu ya mutsi wanda bai sanya an kammala zaben ba, a karamar Hukumar Kunchi sakamakon yan dabar siyasa dauke da makamai.

Suma jam’iyun siyar sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tare da alkawarin jan kunnen magoya bayan su.

Hukumar EFCC da ICPC suma sun lashi takobin yaki da duk wata hanya ta siyan kuri’a da kudi ko wani abu da cewar ba za su amince da hakan ba.

Gamayyar hukumomin tsaro ne dai suka halacci taron wanda aka gudanar a Police Oficers Mess Bompai Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *