Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Nigeria CNG Sun Bayyana Fargaba Kan Tabarbarewar Tattalin Arzikin Kasar.

Spread the love

Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya, CNG, ta bayyana fargaba kan tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya, inda ta yi gargadin cewa salon Lalube cikin duhu da gwamnatin tarayya ke yi na kara ta’azzara manyan kalubalen tattalin arziki ba tare da samar da wata kwakkwarar mafita ba.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja, Shugaban

na kasa, Kwamared Jamilu Aliyu Charanchi, ya ce a halin da ake ciki kimanin ‘yan Najeriya miliyan 133 ne ke fama da Fatara, yayin da miliyan 20 ke fama da rashin aikin yi, inda ya soki manufofin gwamnati na tattalin arziki, dake kuntata rayuwar ‘yan kasa kamar hauhawar farashin kayayyaki da karin farashin man fetur da kuma karin kudin wutar lantarki.

Ya bukaci shugaba Tinubu da ya rushe tawagarsa ta tattalin arziki domin sake fasaltawa, saboda ba su da zurfin fahimtar yanayin tattalin arzikin Najeriya a zahiri.

Bugu da kari, Charanchi ya Caccaki duk wani yunkurin kara farashin man fetur da sunan samar da kudaden aiwatar da sabon mafi karancin albashin ma’aikata, inda ya bayar da shawarar a samar da wasu hanyoyin da za a bi wajen rage almubazzaranci da kuma tsadar tafiyar da gwamnati.

Sai dai ya roki shugaba Tinubu da ya sa kishi da jajircewa wajen magance wahalhalun da al’ummar Najeriya ke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *