Gamayyar kungiyoyin sa kai na Arewacin Nijeriya sun ce rashin shugabanci nagari ne ke haifar da matsaloli a kasar.

Spread the love

Gamayyar kungiyoyin sakai na arewacin Nijeriya sun bayyana cewar, tabarbarewar tattalin arziki da rashin tsaro da Nijeriya ke fuskanta a matsayin rashin iya yafiyar da shugabanci mai inganci.

Wannan na kunshe a wani taron manema labarai da gamayyar kungiyoyin sa kan suka shirya a jahar kano.

Gamayyar kungiyoyin dake da rassa a jahohi 19 ciki harda birnin tarayya Abuja sun bayyana jimaminsu ga me da halin da Al’ummar kasar ke ciki musamman yankin arewa dake fama da matsalar rashin tsaro,sace-sace da dai sauran su.

Shugaban gamayyar kungiyoyin Ambasada Ibrahim waiya, ya bayyana cewar bashin da shugaban kasa Ahmad Bola Tinubu, ke ciyo wa,karuwar rashin tsaro,tabarbarewar tattalin arziki sune abubuwan da ke haifar da koma baya ta kowanne fanni a kasar.

Waiya ya bayyana cewa kafin zuwan sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kimanin mutane milian 130 ne ke fama da talauci a kasar wanda a halin yanzu adadin ya zarce haka.

Ya kara da cewa bayan lalacewar Demokuradiyya an samu karuwar aiyukan ta’addanci kamar safarar kananan yara da mata,garkuwa da mutane da sauransu musamman a jahohin kaduna,Katsina,filato, Niger, sokoto da kuma jahar zamfara.

Kungiyar dai ta bayyana jimamin ta dangane da yadda alkalai ke nema su zama “yan amshin shatan masu rike da mukaman mulki, duba da cewa doka da hukuncin Shari’a Abune Mafi daraja da al’umma ke da yakini akai.

Akarshe kungiyar ta shawarci shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu, da ya duba yiwu war karbar bashi a hanun yan kasuwar cikin gida wanda hakan zai taimaka wajen habbaka tattalin arzikin kasar a fannoni daban daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *