Ganduje Ya Kaurace Wa Zaman Shari’ar Zargin Sa Da Rashawa

Spread the love

Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da iyalansa sun kaurace wa zaman shari’ar da gwamnatin ke zargin su da badakalar kudade.

Gwamnatin jihar mai ci ta maka na zargin Ganduje da iyalansa da wasu makusantansa da cin hanci da rashawa da karkatar da dukiyar al’umma.

ِAna shari’ar ne a Babbar Kotu Mai Lamba Hudu da ke Sakaariyar Audu Bako a Kano, inda aka sa ran gurfanar da Ganduje, wanda kawo yanzu babu tabbacin ko zai halarci zaman da za a fara saurara.

Hukumar yaki da almundahana ta jihar Kano, na zargin Ganduje ne da laifuka guda takwas.

Shugaban hukumar, Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce hukumar ta gano wata badakalar karkatar da kudaden kanana hukumomi Naira biliyan 51.3 a zaman mulkin Ganduje.

Haka kuma hukumar na zargin zargin fitar da kimanin Naira miliyan 600 daga asusun gwamnatin Kano zuwa wani kamfani da tsohon gwamnan yake darakta kuma mai dakinsa ke gudanar da asusunsa.

Muhuyi ya ce sun shirya gabatar da shaidu 15 da kuma hujjojin da ke nuna alakar tsohon gwamnan da laifuffuka da ake zargin sa.

Wasu dai na zargin zargin da hukumar ke wa Ganduje da iyalinsa ramuwar gayya ce kan dakatarwar da ya yi wa shugaban hukumar, amma Muhyi ya musanta zargin da cewa tun Ganduje na mulki hukumar ta fara aiki kan lamarin, wanda shi ne ma dalilin da ya sa aka dakatar da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *