Gani ga wane: Yan sandan Kano sun fara kama matasan da ke tare mata suna yi mu su kalaman batsa na Kin iya Kunu.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano ta cafke wani matashi da ake zargi da bin wata baiwar Allah abaya tare da ce mata ” Kin iya Kunu”, hakan bai yi wa matashiyar dadi ba ,  ta kai korafin sa wajen jami’an yan sanda.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Abdullahi Haruna Kiyawa , ya tabbatar wa da Idongari.ng cewar yanzu haka matashin da bai bayyana sunan sa ba, yana tsare a hannun jami’an yan sandan su, dan amsa tambayoyi kafin daukar matakin da ya dace.

A lokuta daban-daban matasa musamman masu wasan barkwanci, a shafukan sada zumunta ne, ke fito wa da wani abu wanda matasa ke amfani dashi zuwa wasu lokuta.

Sai dai Kalmar Kin Iya Kunu kalma ce ta batsa da matasa Maza da Mata ke furta wa a shafukan sada zumuntar , har ta yadu a bakunan kananan yara, domin kuwa tasha  bamban da wasan barkwanci inda karara kalmar ke nuna fitsara da rashin tarbiya ga ma su furta ta.

A kwai bukatar Malamai da Limaman masallatan juma’a su ci gaba da nusar da matasan kan yin abunda yafi dace wa da su, don cin ribarsa a gobe kiyama , ba yin abun da zai rusa aiyukan su da rayuwar su baki daya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *