Wasannin da za su fi zafi a zagayen ƴan 16 na gasar Afcon 2023

Spread the love

Gasar Kofin Afirka ta 2023 da ake gudanarwa a ƙasar Ivory Coast na gudana cikin ƙayaratwa da abubuwa na ban mamaki.

Bayan kammala wasannin cikin rukuni an samu ƙasashe 16 da suka tsallaka zuwa zagaye na biyu na gasar, wanda za a fara fafatawar a yau, inda ƙasashen ke fatan zuwa zagayen kwata fayinal.

Karawar ta matakin rukuni ta bayar da mamaki kasancewar wasu daga cikin ƙasashen da ake tunanin za su iya lashe kofin sun gaza taɓuka abin kirki.

Ƙasashen da za su buga zageyen gaban su ne Equatorial Guinea da Najeriya da Cape Verde da Egypt da Senegal da Cameroon da Guinea da Angola da Burkina Faso da Mauritania da Namibia da Dr Kongo da Ivory Coast Da Afirka ta Kudu da Moroko dsa kuma Mali.

Tuni dai aka raba jadawalin fafatawar zagayen ‘yan 16n, inda kowace ƙasa ta son abokiyar karawarta.

To sai dai akwai wasu fafatwa da ake ganin za su ja hankalin ‘yan kallo da masu sha’awar ƙwallon ƙafa a wannan zagaye, kamar haka:

Karan wannan labarin: Wacce ƙungiyar tsaro ce Miyetti-Allah ta kafa,kuma mene ne ayyukanta?

Najeriya da Kamaru

Karawa ce da za ta ja hankalin masoya ƙwallon ƙafa a faɗin Afirka, kasancewa yadda duka tawagogin suke da manyan zaƙaƙuran ‘yan wasa da kuma tarihin lashe wannan gasa ta Afirka.

Tawagar Najeriya na da manyan ‘yan ƙwallo da ke taka leda a manyan ƙungiyoyin nahiyar Turai ciki har da gwarzon dan wasan Afirka na 2023, Victor Osimhen da ke taka leda a ƙungiyar Napoli da ke Italiya.

Kamaru kuwa na da tarihin lashe kofin gasar har sau biyar a tarihi, wadda ita ce ƙasa ta biyu bayan Masar da ke da yawan kofunan gasar.

Yayin da Najeriya ta lashe gasar sau uku a tarihi.

Wasan zai ja hankalin ‘yan kallo musamman ganin yadda tawagogin ke da manyan ‘yansa da kuma.

Wasan karshe a gasar Afcon da tawagohgin suka buga tsakaninsu shi ne a shekarar 2019, inda Najeriya ta ci wasan dakyar da ci 3-2.

Tijjani Babangida wanda tsohon dan wasan super Eagles ne ya shaida wa BBC cewa wasa tsakanin Najeriya da Kamaru tamkar wasan ƙarshe yake, domin kuwa a cewarsa duk lokacin da ƙasashen biyu za su kara to wannan wasa daban yake.

“Wasa ne babba, wanda zai yi wahala ma ka iya hasashen wanda zai lashe shi”, in ji shi.

Shi ma ɗan wasan gaban Najeriya Moses Simon ya ce suna sane da yadda Kamaru ke saka karfi wajen buga wasa, yana mai cewa sun tattauna hakan a tsakaninsu ‘yan wasa.

A wani taron manema labarai da ya gudana a birnin Abidjan Simon ya ce “ina ganin karfin jiki ba shi ke kawo nasara ba, mu burinmu shi ne kawai mu cinye su duk da ta hanyar da ta dace.”

Senegal da Ivory Coast

Wani wasan da ke ganin zai ja hankulan masu kallo da sha’awar ƙwallon ƙafa shi ne wasan da za a kara a wannan zagaye tsakanin Senegal da Ivory Coast.

Senegal ta kasance ƙasa ɗaya tilo a gasar da ta yi nasara a duka wasanninta na cikin rukuni, inda ta ja ragamar runukun da makinta tara.

Hakan ne ma ya sa wasu ke hasashen cewa ƙasar ka iya lashe kofin na bana.

Ƙasar na da fitattatun ‘yan wasa da ke taka rawa a nahiyar Turai ciki har da Sadio Mane da ke taka leda tare da Ronaldo a ƙungiyar Al-Nasr ta Saudiyya, sannan ga irin su kalidou koulibaly wanda shi ne kaftin din tawagar.

Haka kuma ƙasar ce ke riƙe da kofin gasar da ta ɗauka a shekarar 2021 da aka gudanar a Kamaru, don haka za ta yi duk mai yiyuwa domin kare kofin nata.

Yan sandan Jigawa sun cafke wadanda ake zargi da satar Awaki 48

A gefe guda kuma ita ma ƙasar Ivory Coast wadda ke karɓar baƙuncin gasar ba kanwar lasa ba ce a fagen wasanni domin tana da tarihi mai kyau a gasar ta Afcon.

Kuma kasancewar a gidanta ake gasar hakan zai ba ta ƙwarin gwiwwa a wasan inda za ta yi ƙoƙarin ganin ba ta kunyata dubban magoya bayanta da za su kalli wasan.

Duk da cewa ba ta taka rawar gani a wasannan cikin rukuni ba, hakan ba zai sanyaya mata gwiwwa ba don ganin ta fitar da kitse daga wuta, ta kuma fita kunyar magoya bayanta.

Moroko da Afirka ta Kudu

Wannan ma wani wasa ne da ake ganin zai ja hankalin masoya ƙwallon ƙafa duba da yadda ƙasashen ke tashe a baya-bayan nan a fagen wasanni.

Moroko ta ƙasance ƙasar Afirka ɗaya tilo da ta taɓa kai wa zagayen dab da ƙarshe a gasar cin kofin Duniya da aka gudanar a Qatar cikin shekarar 2022.

Ƙasar ta bai wa duniya mamaki, musamman yadda ta fitar da manyan ƙasashen Turai – da ke da ƙarfi a fagen tamaula ciki har da sifaniya da Portugal – daga gasar Kofin Duniyar.

Hakan ya sa ake ganin ƙasar za ta taka rawar gani a wannan gasa ta Afcon.

Moroko na da zaƙa-ƙuran ‘yan wasa na gani na faɗa, da suka haɗar da Achraf Hakimi da ke taka leda a PSG da Hakim Ziyech da sauran manyan ‘yan ƙwallo da suka nuna kansu a nahiyar Turai.

Sai dai rabon da ta kofin tun 1976, don haka tana da matuƙar ƙishirwar kofin.

A nata ɓangare ita Afirka ta Kudu za ta yi duk mai yiyuwa wajen ganin ta taka rawar gani a wannan wasa, musamman ganin cewa wasan ne damarta ta ƙarshe ta ci gaba da kasncewa a gasar.

Masar da DR Kongo

Wani wasan da ke ganin shi ma wasa ne mai zafi shi ne wasa tsakanin Masar da DR Kongo.

Masar ta kasance ƙasa da ta fi kowace ƙasa lashe gasar, inda ta lashe kofin har sau bakwai.

To sai dai wani abu da ka iya zama cikas ga ƙasar shi ne batun rashin zaƙa-ƙurin ɗan wasanta da ke taka leda a Liverpool wato Mohamed Salah, wanda ya samu rauni a wasannin cikin rukuni, kuma likitoci suka tabbatar da cewa zai ɗauki lokaci kafin ya murmure.

To amma duk da haka, wanna ba zai sanyaya gwiwwar sauran ‘yan wasan ƙasar ba, waɗanda ke fatan ci gaba da riƙe tarihin da ƙasar ke da shi a gasar.

A ɓangaren DR Kongo kuwa duk da cewa ba ta taɓa lashe kofin ba, hakan ba zai sa ta yi la’asar ba a ƙoƙarinta na kafa tarihi.

Kuma dama a duk lokacin da ƙungiya ke wasa wadda ta fi ƙwarewa, to sai ta fi ƙoƙari ganin cewa abokiyar karwar tata ba kanwar lasa ba ce, to za ta saka ƙarfi don ganin cewa ta taka mata burki, wanda hakan ne kuma zai ƙara wa wasan armashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *