Gidauniyar AMG za ta tallafawa hukumar jin ƙai ta jihar Kano da dabarun gudanarwa

Spread the love

Gidauniyar Aminu Magashi garba ta ci alwashin tallafawa Hukumar jin ƙai da yaƙar talauci a jahar Kano ta ɓangaren Samar da dabarun ci gaba mai ɗorewa.

Jawabin haka ya fito ne daga bakin babban darakta dake kula da aikace-aikace na Gidauniyar, Malam sulaiman Jalo inda ya ce ,ziyayar da Dakta Aminu ya kai ga hukumar jin kƙi da yakar talauci yana da nasaba da yadda yake da kishi jahar sa.

Dakta Aminu, ya gana da kwamishiniyar hukumar Hajiya Amina Abdullahi sani (HOD) inda ya ce , Gidauniyar AMG Na da hange akan ci gaban jahar Kano ta fannin yakar talauci da jin kai wajan Samar da Tallafi ga mata da Matasa, inganta ilimi da lafiya, magance matsalar Tsoro.

Hakazalika, Gidauniyar AMG za ta tallafawa Hukumar wajen shirya taron ga Masu ruwa da tsaki dake jahar Kano akan kudirin Samar da hanyoyin na jin kai tare kula Alaka mai karfi Hukumar jin kai ta kasa, da kuma shirya kuduru na shekara 5 akan dabarun jin kai da yakar talauci a jahar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *