Gidauniyar ci gaban fasahar zamani mai dorewa ( sustainable Technology Development Foundation), ta dasa bishiyu 2,000 a jami’ar Azman da sauran sassa a jahar Kano.
Shugaban gidauniyar ta samar da ilimin fasahar, Kwamared Muhd Sani Takalmawa, ne ya bayyana hakan a wajen Taron dasa bishiyun da aka gudanar.
Kwamared Muhd Takalamawa ya kara da cewa, dasa bishiyun zai rage yawan afkuwar cutuka da kuma kawo ci gaban tattalin arziki Mai dorewa.
Ana ta jawabin shugabar jami’ar Azaman, Farfesa Fatima Batulu Muktar, taja hankalin al’umma da su guji sare bishiyu barkatai don kaucewa zaizayar kasa da kwararowar Hamada.
Farfesa Fatima Muktar, ta ce kasancewar bishiyu da tsirrai na daya Daga cikin Abubuwan ma su muhimmanci a rayuwar dan Adam, musaman wajen shakar iska da kuma Samun yayan Itatuwa ma su kara lafiya ga jikin Dan Adam.
Wakiliyar idongari.ng ta ruwaito cewa,taron ya gudana a harabar babban dakin taro dake jami’ar ta Azman dake kan titin Maiduguri a Kano, Wanda daliban makarantu da kuma manyan Baki daga sassa daban-daban suka halatta.
- SON ta karrama kamfanoni 30 kan samar da kayayyaki masu inganci a Kano
- Masu suka ku yi ta yi ko a jikina – El-Rufai