Gidauniyar Aliko Dangote (ADF) ta kaddamar da shirin rabon abinci na kasa na 2025 da darajarsa ta kai Naira biliyan 16, wanda zai tallafawa ‘yan Najeriya miliyan daya da kayan abinci.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar da aka gudanar a Jihar Kano, Shugaban Gidauniyar, Alhaji Aliko Dangote, wanda diyarsa Maryam Aliko Dangote ta wakilta, ta bayyana cewa shirin yana da burin rage radadin talauci da yunwa a wannnan lokacin.
“Wannan shiri yana nuna tausayawa, hadin kai da kuma kishin al’umma. A cikin wannan mawuyacin hali da kasar ke fuskanta, muna kokarin bayar da gudunmuwa domin rage matsin rayuwa,” in ji shi.
Shirin zai fara ne a Jihar Kano, inda za a raba jakunkuna 120,000 na shinkafa ga talakawa a kananan hukumomi 44 na jihar, kafin a ci gaba da rabawa a sauran jihohin Najeriya.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Mataimakinsa, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya wakilta, ya jinjinawa Dangote bisa wannan gagarumin tallafi da ke nufin kawar da yunwa a kasar.
- Dalilin Da Ya Sanya Rundunar Yan Sandan Kano Ta Karrama Wakilin Muhasa TV & Radio
- An Nada Dagzee Salihu Rano A Matsayin Mai taimakawa Dan Majalissar Dokokin Kano Kan Kafofin Yada Labarai
Shugabar Gidauniyar Aliko Dangote, Zouera Youssoufou, ta ce wannan shiri wani bangare ne na alkawarin da Dangote ya dauka na taimakon al’umma, tare da kira ga sauran ‘yan kasuwa da su bada tasu gudunmuwa don rage wahalhalun da ake fuskanta.
Alhaji Dangote ya bukaci kamfanoni da ‘yan kasuwa su hada kai da gwamnati wajen kawo karshen yunwa, yana mai cewa ya zama dole a hada hannu tsakanin gwamnati da masu zaman kansu don bunkasa jin dadin rayuwar ‘yan kasa.
Wannan shiri yana tabbatar da cewa hadin gwiwar masu zaman kansu da gwamnati na taka muhimmiyar rawa wajen yakarin yunwa da kuma tallafawa mabukata a Najeriya.