Gidauniyar Dangote Ta Raba Buhunan Shinkafa 1m A Nigeria, Da Ciyar Da Mutane 10,000 Kullum A Kano.

Spread the love

Shahararren Attajirin nan na Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ta hannun gidauniyar Aliko Dangote, ya kaddamar da rabon dafaffen Abinci kyauta ga musulmi 10,000 don yin buda baki a watan Ramadan a jahar Kano.

Wannan na kunshe ta cikin Wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’ar yada labarai ta gidauniyar Aliko Dangote, Samira Sanusi a jahar Kano.

Sanarwar ta ce an Kara yawan adadin buhunan shinkafar da aka raba zuwa miliyan daya, wadanda kudinsu ya kai sama da naira biliyan 13, a fadin jahohin Nigeria 36 ciki harda birnin tarayya Abuja.

Gidauniyar Dangote Ta Raba Buhunan Shinkafa 1m A Nigeria, Da Ciyar Da Mutane 10,000 Kullum A Kano.

Wannan dai na zuwa ne bayan miliyoyin Yan kasar sun shiga halin matsin rayuwa , sakamakon tabarbarewar tattalin arziki kara.

Gidauniyar Dangote ta Kara da cewa , ta yi hakan ne domin rage wa al’umma kalubalen tattalin arziki da suke fuskanta.

Haka zalika an kara yawan mutanen da suke amfani da ciyarwar Biredi, a jahar Kano, zuwa dudu ashirin, yayin da jahar Lagos kuma mutane dubu goma sha biyar, Wanda aka faro tun lokacin shekarar 2020 lokacin cutar Covid 19.

Ana dai raba dafaffen abincin a masallatan juma’a, kan hanyoyi, gidan marayu, gidan Yari da sauran sassan jahar Kano.

Kowanne mutum na samun dafadukar shinkafa, Taliya, farar shinkafa, Naman kaji da na Sa, da kuma ruwa da lemon kwalaba.

Daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin ciyarwar gidauniyar Aliko Dangote, Musa Maikatako Tarauni , ya bayyana Farin cikin sa tare da cewa abincin da aka bashi ya taimaka masa wajen shan ruwa.

Mai katako , ya Kara da cewa, wannan abincin zai rage wa al’ummar dake yin buda baki sa ruwan sha kawai, sakamakon matsin tattalin arzikin da Yan Nigeria ke fuskanta.

” ba Zan iya bayyana farin cikin da na ke ji ba” nasan mutane masu Yawa da suke yin buda baki da ruwan sha kawai” Mai katako”.

Hajiya Inna Tukur , ta godewa gidauniyar Aliko Dangote, bisa tallafin ciyarwar da aka bata domin an fitar da ita daga cikin halin rashin Abinci mai dadi.

Wadanda suka amfana da abincin sun yaba sosai , sakamakon yadda dandonon abincin yake da dadi, har suka yi wa ALHAJI Aliko Dangote, fatan alkairi da samun Aljanantul Fiddaus , sakamakon tausayin al’umma da yake nuna wa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *