Gidauniyar Festula Ta Koka Da Gazawar Gwamnatin Kano Na Rashin Samar Da Kayan Aiki Ga Ma Su Lalurar Yoyon Fitsari.

Spread the love

Gidauniyar Fistula Foundation wata gidauniya ce dake samun taimako ko tallafi daga majalisar dinkin duniya da nufin kula da matan da suka tsinci kansu cikin yanayi na kamuwa da lalurar Yoyon Fitsari.

Gidauniyar na aiki tukuru wajen yiwa masu fama da lalurar aiki tare da basu horo kan wasu daga cikin sana’o’I da nufin su rike su wajen dogaro da kai bayan an kammala yi musu aiki sun warke tare da komawa cikin yan’uwansu.

Yawanci gwamnatin Kano kan hada kai da Gidauniyar wajen ganin an tallafawa matan ta wani bangare, misali Abincin da sukan ci a cibiyar kula da su dak unguwar Kwalli, da sauran wasu kayayyakin bukatu na musammn ga masu fama da lalurar.

Duk bayan Wata Uku Gidauniyar Fistula kan gabatar a taron yaye mata daidai gwargwado wadanda suka yiwa aikin lalurar kuma suka warke tar da bsu tallafin jari, ko keken dinki, ko injin taliya, ko markade, da sauransu.

A INA MATSALAR TAKE?

Majalisar dinkin duniya ta wajabta cewa dole ne duk fadin duniya aiki ya zama kyauta ga masu fama da lalurar Yoyon Fitsari, a kokarin ganin an rage musu radadi dangne da halin da suka tsinci kansu.

Kuma a duk fadin Najeriya kamar yadda shugaban Gidauniyar Fistula Nigeria Musa Isa, ya shaida mana ko ina kyauta ake aiki ga masu annan lalurar, amma abun kaico shi ne yadda a jihar Kano matan da za a yiwa wannnan aiki suke sayen kayan aikin da kudinsu bayan gazawar gwamnatin jihar na samar da kayan bukata ga aikin.

Musa Isa ya ha kiraye kiraye tun zamanin tsohuwar kwamshinar mata ta jihar Kano Dr Zahra’u Muhammad kan gwamnati ta samar da kayan aiki domin aiki ya zama kyauta ga mata masu fama da wannan lalurar amma abu ya gagara.

Bayan zaben 2023, an samu sabuwar gwamnati ta Abba Kabir Yusuf a fatan ganin a ta sauya zani, amma abun ya zama abun kaico domin kuwa itama yanzu haka sama a shekara aya da zuwan ta ko da Allurar Aiki ta gaza samarwa kyauta ga bangaren masu fama da lalurar dake asibitin kararru na Murtala.

Ranar 25 ga watan Yuli, 2024, rana ce da gidauniyar Fistula ta yaye mata 50 da suka warke daga cutar bayan aiki, anan ma Musa Isa ya sake jaddada kira ga gwamnatin Kano kan ta yi kokarin samar da kayan aikin a asibitin Murtala Muhammad.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin kan ta taimaka wajen sake daukar wasu Likitoci biyu aiki domin ci gaba da kula da masu fam da cutar, kasancewar sun dab da Ritaya.

An taki sa’a a wannan karon domin kuwa Kwamashinar ma’aikata Mata ta jihar Kano Hajiya Aisha Lawal Saji ta halarci wajen da kanta ba sako ba, tare da alkawarin cewa zasu kawo karshen kalubalen da mata masu fama da lalurar Yoyon Fitsari ke fusknta kamar yadda na baya ke daukar alkawarin kawo karshe amma har yanzu ga gaza sauya zani.

Abun jira a gani shi ne ta Inda Hajiya Saji za ta kafa tarihi wajen kawo karshen matsalar sayen kayan aiki ga matan dake fama da lalurar Yoyon Fitsarin a jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *