Gidauniyar Festula ta Najeriya, dake tallafawa mata masu fama da yoyon fitsari (VVF), ta ba da tiyata kyauta da tallafin sana’o’in dogaro da kai ga mata 100 da ke fama da larular Yoyon Fitsari a Jihar Kano.
An gudanar da tiyatar a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.
An yi wa mata 100 da aka zaɓa tiyata don gyara yoyon fitsari, wanda yawanci ke faruwa ne sakamakon tsawaita lokacin haihuwa da wahala, musamman a yankunan da auren kanana da ƙarancin damar samun lafiya.
Shugaban gidauniyar, Alhaji Musa Isah Baba Musa, ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kano da ta ƙara himma wajen yaƙar VVF ta hanyar samar da kayan aikin tiyata kyauta da kayan sana’a ga wadanda suka tsira.Wannan zai rage wulakanci kuma zai ƙarfafawa masu Cutar dawo cikin al’umma.
Masana lafiya sun nuna auren wuri a matsayin babban sanadin yoyon fitsari a Arewacin Najeriya.
- Abba ya karrama fitattun Kanawa 35
- Waiya ya kaddamar da kungiyar masu tallata aiyukan gwamnan Kano a Facebook
Jihar Kano ta ci gaba da kasancewa cikin yankuna masu fama da wannan cuta, duk da cewa hukumomi sun ce an fara samun raguwar lamuran.
Yawancin wadanda suka samu Cutar VVF suna fuskantar saki, watsi da su, ko warewa daga al’umma saboda rashin fahimtar cutar.
Gidauniyar ta jaddada bukatar magance wannan kyamar a cikin al’umma.
Najeriya tana da mafi yawan mata masu fama da yoyon fitsari a duniya, musamman saboda al’adun gargajiya kamar auren wuri da rashin isasshen kula da lafiyar uwa da jariri.
Wannan shiri ya nuna rawar da ƙungiyoyi masu zaman kansu ke takawa wajen magance matsalolin lafiya da zamantakewa a yankunan da ba su da isassun ayyuka.
Duk da haka, ci gaba da taimakon gwamnati, inganta ababen more rayuwa na lafiya, da wayar da kan jama’a game da haƙƙin mata su ne mabuɗin kawar da yoyon fitsari da tallafa wa wadanda suka tsira na dogon lokaci.