Gidauniyar Tallafa Mata Ma Su Yoyon Fitsari ( Festula Foundation) Ta Koka Kan Rashin Yi Wa Mata Aiki Kyauta A Kano

Spread the love

Gidauniyar tallafa wa mata masu lalurar yayon fitsari ta Festula Foundation of Nigeria, ta yi bukaci gwamnatin jahar Kano ta samar da kayan aikin da za a dinga yi wa mata, ma su fama da yoyon fitsari aiki kyauta, don rage mu su radadi daga kyamar da ake nuna mu su.

Shugaban gidauniyar Alhaji Musa Isah, ( Baba Musa), ne ya bayyana hakan a jiya Asabar, yayin gudanar da taron da festula Foundation , ta saba shirya a unguwar Kwalli Kano, don tuna wa da mata ma su fama da lalurar, kamar yadda majalissar dinkin duniya ta ware kowacce ranar 23 ga watan Mayu don gudanar da bikin.

Alhaji Musa Isah, ya ce wannan lokacin ba su samu damar gudanar da taron a ranar da majalissar dinkin duniya ta ware ba, saboda suna da rassa a jahohin Nigeria 19, wadanda suka ziyarci wasu daga ciki don gudanar da taron, shi yasa suka kara kwana biyu akan ranar da aka saba yin bikin ranar.

Ya kara da cewa a kowacce shekara suna tara mata ma su lalurar don wayar da jama’a kai, dangane da abunda yake haifar da yoyon fitsari.

Baba Musa ya shaida wa, jaridar idongari.ng, cewa a wannan shekarar ta 2024, sun gayyaci mata 100 zuwa wajen taron, amma sun sami mata sama da 217 wadanda suka zo daga sassa daban-daban.

Sai da ya ce matan an yi mu su aiki kyauta, kuma sun warke yayin da wasu kuma za a sake yi mu su aikin don su samu waraka baki daya.
A cewar sa gwamnatin jahar Kano tana bada gudunmawa sosai, amma suna fama tarin matsalolin, kamar rashin yi wa matan aiki kyauta har sai sun biya kudi , wanda a tsarin da MDD ta fitar duk macen da ta kamu da yoyon fitsari za a yi mata aiki kyauta ba tare da ta biya kudi ba.

Kwamishiniyar mata ta jahar Kano Hajia A’isha Saji Rano,Wadda ta samu wakilcin Daraktar walwalar mata,a ma’aikatar, Binta Muhamed Yakasai, ta bayyana cewa suma wannan abu yana damunsu tsawon shekaru uku da suka gabata amma tuni sun dauki hanyar warware matsalar tare da hadi gwiwar ma’aikatar lafiya ta jahar Kano.

Binta Yakasai, ta kara da cewa suna da wajen koyar da matan sana’o’in dogaro kai , kuma akwai kwararru wadanda suke horas da su yadda yakamata.

Koda a ranar 27 ga watan Janirun 2024 , Festula Foundation of Nigeria, ta yi wa mata 50 aiki kyauta tare da horas da su, sana’o’in dogaro da kansu bayan sun koma gida.


Matan da aka koyar da su sana’o’in na daga cikin matan da Festula Foundation, tare da hadin kan ma’aikatar mata ta jahar Kano, suka kula da lafiyar su har suka warke a cibiyar dake Unguwar Kwalli Kano.

Shugaban gidauniyar Alhaji Musa Isah, ya yi kira ga gwamnatin jahar , ta yi hobbasar samar mu su da kayan aikin da za a dinga yi wa matan aiki kyauta , domin yawancin ma su fama da lalurar ba su da kudin da za su biya a yi musu aikin, inda ya ce wasu daga cikin al’umma tsangwamarsu suke yi, kuma suna tsintar kansu a cikin damuwa sakamakon tsangwamar da ake yi mu su .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *