Gobara ta tashi a Babban Ofishin ’yan sanda da ke unguwar Dakata a Karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Muhammed Usaini Gumel, ya ce gobarar ta safiyar Litinin, “ta kone wani bangare gaba daya a babban ofishin ’yan sandan da ta tashi.
“Amma duk haka, babu abin da ya sami makaman da ke ofishin.”
karan ta wannan labarin Hukumar Karbar Koke-Koke Ta Rufe Rumbunan Abinci 5 A Kano
Kwamishinan ’yan sandan ya ce tashin gobarar ke da wuya, jami’an hukumar kashe gobara ta jihar suka zo suka kashe ta, kuma ana bincike don gano musabbabin tashinta.
“An killace wurin domin hana masu kallo da miyagu shiga, kuma DPO na yankin yana kan tantance wasu takardun da abin ya shafa,” inji shi.