Gobara Ta Tashi A Gidan Tsohon Gwamnan Jihar Kano

Spread the love

Gidan tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau da ke unguwar Mudubawa a yankin Karamar hukumar Nassarawa ya kama da wuta wacce ta cinye Kayayyaki a dakin matarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta faro ne daga dakin girki na matar gwamnan Hajiya Halima Shekarau.

Har ya zuwa yanzu dai ba tabbatar da musabbabin faruwar lamarin ba

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun tsohon Gwamnan Malam Sule Ya’u Sule ya ce anyi sa’a gobarar ta shafi dakin tsohon Gwamnan ne kawai a gidan.

” Mun gode Allah iya daki daya ne kawai gobarar ta shafa kuma cikin hukuncin ubangiji an jami’an hukumar kashe gobara ta jihar kano sun kashe wutar”.

Shi ma Mai Magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar kano Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, Amma yace ba zai iya cewa komai kan lamarin a yanzu ba.

” Tabbas gobara ta tashi a gidan tsohon gwamnan, kuma yanzu haka jami’anmu suna aiki don ganin sun dakatar da wutar don gudun kar wutar ta kara yaduwa”. A cewar Saminu Yusuf

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *