Hukumar Dake Rarraba hasken Wutar Lantarki ta shiyyar kano ta tabbatar da tashin Gobara a Tashar Lantarki dake Unguwar Ɗan Agundi dake Birnin Kano.
Kakakin Hukumar Rarraba hasken Wutar Lantarki (TCN) na shiyyar kano Adam Umar ne ya tabbatar da hakan a zantawar sa da jaridar Gtrhausa, inda ya ce bazai iya cewa komai ba akan batun har sai sun gama tattara bayanai.
Watan Ramadan: Hukumar Tace Fina-finai Ta Bada Umarnin Garkame Gidajen Gala A Jahar Kano
Tashar Lantarkin na cikin manyan tashoshin Lantarkin Dake bawa kwaryar birnin Jihar Kano wutar lantarki, lamarin da wasu ke ganin Akwai yiwuwar a daɗa samun ƙarancin Wutar a sakamakon wannan Gobara.
Kuma Gobarar na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake shirye-shiryen fara Azumin Watan Ramadan a gobe Litinin ko kuma a jibi Talata idan watan ya cika Talatin.