Gurfanar Da ƙananan Yara A Gaban Kotu Tsantsar Zalunci Ne — Atiku.

Spread the love

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya soki Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan abin da ya kira zalunci dangane da gurfanar da ƙananan yara a gaban kotu domin yi musu shari’a.

A wannan Juma’ar ce wani bidiyo ya nuna wasu ƙananan yara aƙalla 20 kwance a zauren kotu suna numfashi da ƙyar da ke alamta yunwa ta yi musu illa.

Tsananin Yunwa Da Wuya Ta Sanya Yaran Da Ake Zargi Da Zanga-zangar Yunwa Sun Suma A Kotu.

Sai dai cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa X, tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ya ce ya damu da bidiyon yaran da aka nuna “bayan yunwa ta yi musu illa, a inda aka tsare su.”

 

Wannan abu na tayar da hankali ya tuna min da zaluncin ’yan aƙidar Nazi, tare da ƙara fito da yadda gwamnati ke nuna rashin kulawa da rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, musamman ƙananan yara”, in ji Atiku.

Ya ce Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bai wa ƙananan yara cikakken ’yancin mutuntawa, amma abin mamakin sai suka rasa hakan a Najeriya, a cewar Atikun.

Bidiyon yadda Yara suka Sume a kotu

“Ina mamakin mutumin da ke iƙirarin kare dimokuraɗiyya, har ya jagoranci zanga-zanga a baya, amma a yanzu yake barazana ga waɗanda ke yunƙurin nuna damuwarsu kan halin da suka shiga sakamakon manufofinsa masu tsauri.”

Ya ƙara da cewa ƙananan yaran waɗanda su ne suka fi cutuwa kan manufofin gwamnatin Tinubun na da damar gudanar da zanga-zangar lumana kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba su dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *