Mu na Nema wa Gwamna Abba kabir Yusuf Afuwa daga Wajen Mal Ibrahim Aminu Daurawa-Rabiu Kiru.

Spread the love

Daga Nazifi Bala Dukawa

An bukaci gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf da ya nemi
afuwar Mallam lbrahim Daurawa amadadin al’umar jihar kano
sakamakon abinda ya faru.

Guda daga cikin Datawan karamar hukumar kiru a jahar Kano,Rabiu Koru ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gana wa da manema labarai.

Rabiu Kiru ya kuma tabbatar wa da Mallam lbrahim Daurawa cewa
tafiyarsa za ta kawo karshen al’amarin.

Kiru ya kuma bayyana cewa faruwar al amarin aiki ne na shaidan
wanda yayi fatan ba zai sake faruwa ba anan gaba.

Hukumar Hisbah a Kano Ta Kamo Mata da Maza a gidajen Rawar Solo.

Ta Inda Baki Ya Karkata Ne Ya Sanya Sheik Aminu Daurawa Ajiye Mukaminsa

Kiru ya kasance daya daga cikin na hannun daman jagoran darikar
kwankwasiyya Injiniya Rabiu Musa Kwonkwaso inda ya kuma
bukaci al’umar jihar kano da su yafe wa gwamna Abba Kabir Yusif
bisa abinda ya kira kuskuren harshe.

Daga nan sai ya nemi ci gaba da bayar da goyon baya daga al’umma, ta bangaren yin amfani da damar neman hadin kan
daukacin yan jarida da kafafen yada labaran dake jihar don warware matsalar.

Murabus ɗin malamin na zuwa kwana guda bayan da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwarsa kan salon da hukumar Hisbah ke bi wajen yaƙi da masu aikata baɗala a Kano.

A wani bidiyo mai tsawon ƙasa da minti uku da Sheikh Daurawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, malamin ya bayyana cewa kalaman gwamnan sun kashe masa gwiwa kuma a don haka ya ajiye muƙaminsa na jagora a hukumar ta Hisbah.

Daurawa ya ce “Mun yi iya ƙoƙarinmu domin yin abin da ya kamata, to amma ina bai wa mai girma gwamna haƙuri bisa fushi da ya yi da maganganu da ya faɗa. Kuma ina roƙon ya yi mani afuwa na sauka daga wannan muƙami da ya bani na shugabancin Hisbah.”

A ƴan kwanakin da suka gabata ne, Hisbah ta kama shahararriyar ƴar tiktok ɗin nan, Murja Ibrahim Kunya bisa zargin aikata baɗala a jihar Kano lamarin da hukumar ta ce ke lalata tarbiyyar matasa.

Hukumar ta kuma aika ta zuwa kotu wadda kuma ta tura ta gidan gyaran hali.

Bayan an aika ta gidan gyaran hali ne kuma aka wayi gari da labarin sakinta daga kurkuku, abin da ya yi ta tayar da ƙura a tsakanin al’ummar jihar inda wasu ke ganin da hannun gwamnati a sakin nata – zargin da gwamnatin ta musanta.

A yanzu dai Murja Kunya na asibitin masu larurar ƙwaƙwalwa bisa umarnin kotu domin gwada lafiyar ƙwaƙwalwarta. Kotun ta ce ƴar Tiktok ɗin za ta yi wata uku a can.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *