Fursunoni Sun Tsere Daga Gidan Yarin Comoros

Spread the love

Hukumomi a Comoros sun ce gomman fursunoni sun tsere daga gidan yarin da ke birnin Maoroni, inda suka fice ta kofar gidan yarin.

Mai gabatar da kara na kasar, Ali Mohamed Djounaid, ya ce 38 ne suka tsere daga gidan yarin mafi girma.

Sai dai ya dora laifin ne kan jami’an tsaro da ya ce sun yi sakaci.

Mai magana da yawun gwamnati ya ce akwai alamun da ke nuna an dade da kitsa tserewar fursunonin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *