Gwamna Abba Kabir da manyan mutane za su halarci auren ’yar Sanata Kwankwaso a Kano

Spread the love

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai bayar da auren ’yar jagoran Kwankwasiyya, Dokta Aisha Rabiu Musa Kwankwaso ga Injiniya Fahad Dahiru Mangal a ranar Asabar.

Dokta Aisha, ita ce ’yar autar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wadda za ta auri Injiniya Fahad, ɗan attajirin ɗan kasuwar nan na Jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal.

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanar da cewa za a ɗaura auren a ranar Asabar, inda ake sa ran manyan mutane za su halarci ɗaurin auren.

A cikin wata sanarwa, ya ce, “Iyalan biyu suna farin cikin gayyatar abokai, ’yan uwa, abokan siyasa, ’yan kasuwa, shugabannin addinai da na gargajiya don halartar bikin da za a yi a Fadar Sarkin Kano, da ke Ƙofar Kudu.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Muna gayyatar abokai da abokan siyasa daga kowane fanni don halartar bikin auren ’yarmu, Dokta Aisha Rabi’u Musa Kwankwaso da angonta, Injiniya Fahad Dahiru Mangal.

“Za a ɗaura auren a Fadar Sarkin Kano, Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II, da ke Ƙofar Kudu a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2024 da misalin ƙarfe 11 na safe.”

Bature, ya ƙara da cewa ana sa ran manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya da za su halarci ɗaurin auren.

Ya kuma buƙaci hukumomin tsaro su tabbatar da sun lura da zirga-zirgar ababen hawa daga Gidan Gwamnatin jihar zuwa Fadar Sarkin Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *