Gwamna Abba Kabir ya bullo da Ayukan Cigaba a fadin Jihar Kano-MD ARTV

Spread the love

Daga Rabiu Sanusi

Mukaddashiyar Shugabar gudanarwar gidan Talabijin na Abuubakar Rimi dake jihar Kano, Hajiya Hauwa Isah Ibrahim ta bayyana Gwamna Abba Kabir matsayin shugaba mai kishin Jama’ar shi.

Hajiya Hauwa ibrahim ta bayyana hakane a ranar larabar nan a wata ziyarar murna da rukunin Yan Jaridu na fadar gwamnati ta kai mata.

Hajiya Hauwa ta ce a cikin ayukan da gwamna Abba Kabir yayi akwai su masu tarin yawa musamman yadda ya dauki bangarori daba-daban.

Wasu daga cikin ayukan da Hauwa Ibrahim ta bayyana sun hadar da Batun habbaka harkokin ilimi tare da samar da kayan aiki daban daban ga makarantu tare da su kansu malaman.

“Akwai ayuka daban-daban da suka hada da bada unifoam,littatafai,takalma, biyan kudin makarantu, ga dalibai tare da biyan kudin jarabawa.”

Mukaddasshiyar ta kara da cewa gwamna Abba Kabir ya yi kokari matuka wajen Auren Gata, tare da kokarta tura Dalibai zuwa kasashen Ketare domin gudanar da karin karatun su da sauran abubuwa daban-daban.

Takuma yi tsokaci a irin ayukan rabon tallafi da bada jari da, tare da tallafin kayan Abinci ga dumbin al’ummar jihar Kano a lokuta mabanbanta da yayi dan tallafa ma al’umma.

Sai dai Hauwa Ibrahim Isah ta bukaci sauran al’umma musamman Yan Jarida tasu cigaba da bata shawarwari wajen tabbatar da ayukan ta bisa gaskiya da rikon amana.

Kazalika tace amadadinta da sauran ma’aikan wannan gidan Talabijin suna taya maigirma Gwaman murnar cika shekara daya kan kujerar shugabancin wannan jiha mai Albarka.

Shima a nashi jawabin daraktan wayar dakai na fadar gwamnatin Kano Malam Aliyu Yusuf ya bayyana cewa wannan lokaci ne da zata cigaba da kamanta amana dan dawo da martabar wannan Gida.

Aliyu Yusuf ya kuma yi mata addu’o’in samun nasara da fatan sauke nauyin da Allah ya dora mata bisa gaskiya da rikon amana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *