Gwamna Abba Kabir Ya Nada Sabon Sakataren Gwamnatin Kano

Spread the love

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar Kano (SSG).

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a Asabar dinnan.

Nadin Ibrahim zai fara aiki daga ranar Litinin 10 ga Fabrairu, 2025.

Sanarwar ta ce, an zabi Ibrahim ne bisa gogewar da yake da ita, wanda ake sa ran zai yi amfani da ita wajen inganta harkokin gwamnatin jihar Kano.

Umar Farouk Ibrahim, ya kwashe sama da shekaru talatin yana aikin gwamnati , don haka ake fatan zai kawo cigaba sosai a sha’anin tafiyar da harkokin aikin gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *