Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar da jawabinsa karon farko ga Kanawa bayan hukuncin kolin koli

Spread the love

Gwamnan jahar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya bayyana kudirin gwamnatinsa na kyautata rayuwar mutanen jahar, musamman matasa don samar mu su da sana’o’in dogaro da kai don yaki da zaman banza dake jefa matasa harkar shaye-shaye da daidai sauran su.

Gwamnan ya bayyana hakan ne, a jawabin da ya gabatar wa al’ummar jahar Kano cikin daren Lahadi , a filin wasa na Mahaha dake kofar Na’isa.

Abba Gida-gida ya taso daga jahar Kaduna tunda misalin karfe 9:00am na safiyar lahafi , zuwa jahar Kano, amma yawan jama’a ya sanya shi kawa dare kafin ya gabatar da jawabin nasa.

A kalla dai gwamnan ya shafe a wannan 9 akan hanya saboda yanayin tafiyar da ake yi a hankali.

TALLA

Gwamnan Kano ya ce , fanni ilimi zai dawo da karsashin sa, Noma da kuma fannin lafiya don al’ummar jahar su amfana da rokon Damukuradiya da ake bayyana wa.

A jawabin nasa ya godewa al’ummar Kano, Nijeriya da duniya baki bisa addu’o’in da suka yi har aka samu nasara a kotun koli.

Haka zalika ya godewa alkalan kotun koli bisa kamanta gaskiya da suka yi a hukuncin da suke yanke , suka barwa al’umma abinda suka zaba.

Ya kuma godewa shugaban kasa Bola Ahmed Tunibu, da mataimakinsa Kashim Shatima , da suka bari bangaren shari’a ya yi aikin sa ba tare da tsoma baki ba.

Suma jami’an tsaro sun shiga kunshin godiyar gwamnan jahar Kanon, bisa namijin kokarin da suka nuna wajen kare lafiyar al’ummar Kanawa da dukiyoyinsu a koda yaushe.

Ya kuma godewa jagoran kwankwasiyya Engr. Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da yadda ya jajirce har aka samu nasarar da ake kai a halin yanzu.

Gwamna Abba Kabir , ya kara da cewa, akwai wani shiri da suka fito da shi na karbar shawarwari daga al’umma kan abinda ya dace a yi da kuma bai kamata a yi ba.

Sannan ya ce za a ajiye a kwanatinan karbar shawarwarin adukkan mazabu dake fadin jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *