Gwamna Buni ya dakatar da shugaban karamar hukumar saboda rashin da’a a Yobe

Spread the love

Gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da dakatar da shugaban karamar hukumar Machina , Idrissa Bukar-Machina.

An rantsar da Bukar-Machina tare da sauran shugabannin  kananan hukumomi 16 a ranar 10 ga watan Yuni 2024.

Sakataren gwamnatin jihar, Baba Mallam-Wali, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, da ya raba wa manema labarai, a ranar Talata a Damaturu, ya ce an dakatar da shugaban ne saboda rashin da’a.

An kuma umarce shi da ya mika al’amuran karamar hukumar  ga mataimakinsa.

Gwamna Buni Ya Dakatar Da Shugaban karamar Hukuma Saboda Rashin Da’a A Yobe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *