Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawan, ya yi ta’aziyyar dakarun askarawan jihar da ƴanbindiga suka kashe a ranar Litinin.
Gwamnan ya yi ta’aziyar ce a ranar Talata, bayan ƴanbindiga sun kashe askarawan a wani kwantar ɓauna da suka musu ranar Litinin a wani shingen tsaro a yankin Tsafe.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, gwamnan ya bayyana kisan da dabbanci, sannan ya yaba wa jajircewar askarawan tsaron bisa sadaukarwar da suke yi wajen kare rayukan mutane da tasu rayuwar.
“Na samu labarin kashe jami’anmu na askarawa a Tsafe masu suna Nasiru Aliyu da Jabiru Hassan da Abdullahi Dangude da Bashar Bawa da Mu’azu Musa da Anas Dahiru da Anas Yakubu da Lawali Yunusa da wani guda ɗaya.
“Wannan kisan ba komai ba ne face dabbanci, daga ƴanbindiga da suke guje-guje saboda cigaba da farautarsu da jami’an tsaro suke yi.
“Sojoji za su cigaba da farautarsu domin samar da zaman lafiya a jihar da ma yankin baki ɗaya. Ina ta’aziya ga iyalan waɗanda suka rasu da ma mutanen Zamfara baki ɗaya. Ba za mu manta da sadaukarwar da suka yi ba. Allah ya ba waɗanda suka ji rauni sauƙi,” in ji shi, sannan ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta cigaba da tallafa wa iyalan waɗanda suka rasu.