Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya naɗa Omobayo Marvellous Godwin a matsayin mataimakin gwamnan jihar.
Matakin ya zo bayan tsige Philip Shaibu da majalisar dokokin jihar ta yi a zaman ta na yau Litinin.
Omobayo, mai shekara 38 ya yi karatu a fannin injiniya kuma yana da ƙwarewa a ɓangaren mai da iskar gas.
Omobayo ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilai ƙarƙashin jam’iyyar Labour a zaɓen 2023.
Majalisar dokokin jihar ta tsige tsohon mataimakin gwamnan Edo ne saboda ƙin amsa gayyatar kwamitin mutum bakwai da ke bincikensa kan zarge-zargen aikata ba daidai ba.
- Kotu ta tura jami’in Binance gidan gyaran hali na Kuje
- Rundunar Yan sandan Kano, Ta Karbi Shawarwari Daga Masarautun Jahar da Malaman Addini Don Bayar Da Cikakken Tsaro A Bukukuwan Sallah.