Gwamna Obaseki ya zaɓi sabon mataimaki

Spread the love

Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya naɗa Omobayo Marvellous Godwin a matsayin mataimakin gwamnan jihar.

Matakin ya zo bayan tsige Philip Shaibu da majalisar dokokin jihar ta yi a zaman ta na yau Litinin.

Omobayo, mai shekara 38 ya yi karatu a fannin injiniya kuma yana da ƙwarewa a ɓangaren mai da iskar gas.

Omobayo ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilai ƙarƙashin jam’iyyar Labour a zaɓen 2023.

Majalisar dokokin jihar ta tsige tsohon mataimakin gwamnan Edo ne saboda ƙin amsa gayyatar kwamitin mutum bakwai da ke bincikensa kan zarge-zargen aikata ba daidai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *