Gwamnan Filato ya bayar da umarnin rufe makarantar da ta rufta da ɗalibai

Spread the love

Gwamnan jihar Filato, Caleb Matfwang ya bayar da umarnin gaggauta rufe makarantar Saints Academy, bayan ruftawar wani ginin makarantar mai hawa biyu ya kashe ɗalibai 22 ranar Juma’a.

Yayin da yake jawabi a lokacin ziyarar da ya kai makarantar ranar Asabar, Gwamna Matfwang ya ce matakin ya zama dole domin kwantar wa jama’a a hankalin kan firgicin da suka shiga sakamakon ruftawar ginin.

Gwamnan ya kuma jajanta wa iyayen yaran da suka rasa ‘ya’yansu a iftila’in.

Haka kuma ya bayar da umarnin kama duk masu sana’ar haƙar ma’adinar da ke kewayen makarantar.

Makarantar dai na kusa da wata ƙorama da ta yi ƙasa saboda da zaizayar ƙasa.

Mazauna yankin sun ce masu haƙar ma’adinai sun jima suna sana’arsu a yankin tun kafin kafa makarantar.

‘Yan sanda sun ce kimanin ɗalibai 154 ne suka maƙale ƙarƙashin ginin da ya ruftar, lokacin da suke tsaka da rubuta jarrabawa. Inda aka kuɓutar da 132 waɗanda a yanzu ke samun kulawar likitoci a asibitocin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *