Gwamnan jahar Naija, Umaru Bago, ya ba da umarni ga jami’an tsaro su harbe duk dan Dabar da yake dauke da makami ko, ya Yi yunkurin kawo rashin zaman lafiya a jahar.
Gwamna Bago, ya bayyana hakan a wajen bikin sallah , wanda tsohon gwamnan jahar Banbangida Aliyu, ya shirya a Minna Babban birnin jahar.
Umaru Bago, ya bayyana takaicinsa kan yadda yan dabar suka Fara wuce gona da iri a sassan jahar wajen jikkata wadanda ba su ji ba , ba su gani koma su rasa ransu baki daya.
Ma su sharhi kan al’amuran yau da kullum na ganin daukar wannan mataki zai taimaka matuka wajen dakile harkar Daba, da ake ganin rashin daukar tsattsauran hukunci ne ya Kara ta’azzara lamuran.
- Mutane 3 Sun Rasu An Jikkata 10 A Rikicin Sojoji Da ’Yan Keke NAPEP A Yobe
- Shugaban ƙasar Chadi ya fara yaƙin neman zabe