Gwamnan jahar Ondo Rotimi Akeredolu, ya mutu a wani asibiti a jahar Lagos da kudancin Nijeriya.
Rahotanni na cewa, gwamnan ya mutu ne sakamakon tsawon lokacin da ya dauka yana jinyar cutar Daji.
Akeredolu ya mutu ne da misalin karfe 2:00pm na daren ranar laraba a asibitin da yake jinya.
ya mutu yana da shekaru 67 a duniya.
A baya dai ya shafe tsawon watanni uku a kasar Jamus sakamakon fita da ya yi domin duba lafiyarsa, inda daga baya ya dawo gida Nijeriya.